IQNA

Kisan Gilla A kan Musulmi 25 A Afirka Ta Tsakiya

23:44 - October 14, 2017
Lambar Labari: 3482000
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan ta’adda kiristoci masu dauke da makamai sun afkla kan wani masallacia yankin Kimbi na Afirka ta tsakiya inda suka kasha masallata 25 a cikin masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalti daga shafin yada labarai na alkhaleej.ae cewa, Abdulrahamn Borno shugaban majalisar shawara ta musulmi a yankin Kimbi ya sheda ma manema labarai cewa, a jiya Juma’a ‘yan ta’adda na anti Balaka sun kaddamar da hari a yankin inda suka yi kisan gilla kan msuulmi a lokacin salla.

Ya ce ‘yan ta’adda sun fara yanka limamin masallacin ne a gaban jama’a a cikin masallaci, daga nan kuma suka yanka ratibi, bayan nan kuma suka kasha masallata ashirin da uku.

Ya ci gaba da cewa wannan shi ne irin abin da wadannan ‘yan ta’adda na anti balaka suke yi, inda sukan kai farmaki a kan kauyuka tare da kasha dukkanin musulmi da suka sau a wurin tare da wawushe musu dukiya.

Tun a cikin shekara ta 2012 kasar take fama da matsaloli na siyasa, wanda daga bisani ya rikide ya koma na addini, inda musulmi marassa rinjaye suke fusknatar kisan kiyashi.

A cikin shekara ta 2016 an dan samu zaman lafiya, amma daga farkon watan Afirilun wannan shekara, tashin hankali ya sake dawowa a kasar.

3652446


captcha