IQNA

Malamin Addinin Kirista Ya Musulunta A Kenya Ya Mayar Da Majami’arsa Masallaci

23:38 - October 15, 2017
Lambar Labari: 3482001
Bangaren kasa da kasa, wani malamin addinin kirista ya muslunta akasar Kenya, inda ya mayar da majami’arsa masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na The Nairobian cewa, Charles Akwani malamin addinin kirista ne a kasar, wanda kuma bayan musluncutarsa ya mayar da majami’arsa wurin salla da iabada ta addinin muslunci.

Ya ce ya karbi addinin muslunci bayan ya yi nazari da mudala’a, da kuma ganawa da musulmi da yin tambayoyi ga malamai kan abubuwa da dama da yake dea ukatar amsa akansu dangane da addinin muslunci.

Irin bayanan da ya samu sun gamsar da shi kan cewa, lallai addinin muslunci shine addinin gaskiya, wanda ya aye gurbin addinin annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gare shi.

Charles ya muslunta ne a ranar 26 ga watan satumban da ya gabata inda ya wasu daga cikin mabiyansa suka karbi addinin muslunci kuma suke yin salla tare da shi a wurin.

Kasar Kenya dai tana daga cikin kasashen nahiyar Afirka da mafi yawan jama’arsu kiristoci ne, inda adadin suulmi bai wuce kashi goma cikin dari ba.

Da dama daga cikin musulmin kasar dai suna zaune ne a yankin Mombasa, wanda daya ne daga ikin yankna masu albarkatu na kyawun yanayi da kasar noma da kuma jan hankulan masu yawan bude ido.

3652764


captcha