IQNA

Ayatollah Hakim: Raya Taruka Kan Imam Hussain (AS) Dama Ce Ta yada Koyarwar Ahlul Bait

23:22 - October 16, 2017
Lambar Labari: 3482004
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Sayyid Muhammad Sa’id Hakim daya daga cikin manyan malaman shi’ar Ahlul bait (AS) a Najaf ya bayyana cewa, raya taruka da suka shafi Imam Hussain (AS) dama ce ta yada koyarwar ahlul bait (AS).

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Nun ya baya da rahoton cewa, a lokacin da yake ganawa da masu ziyarar a hubbaren Imam Hussain (AS) Ayatollah Sayyid Muhammad Sa’id Hakim daya daga cikin manyan malaman shi’ar Ahlul bait (AS) a Najaf ya bayyana cewa, raya taruka da suka shafi Imam Hussain (AS) dama ce ta yada koyarwar ahlul bait (AS) da hakan ya hada da kyawawan dabi’u, hada kan al’ummar msuulmi, gaskiya, kyautata wa iyaye, hakuri da yarda da lamarin Allah.

Ayatolalh Hakim ya ce wadannan suna daga cikin dabi’un Imam Hussain da kuma saura limamai na ahlul bait, wanda idan da za a yi koyi da su, to da duniya ta zauna lafiya, da ba a ji rikici tsakanin musulmi ba, domin kuwa ahlul bait sun koyar da hakuri a aikace da yin afuwa da yin riko da ibada ta wajibi da kuma ta mustahabbi, yada kauna da son juna a tsakanin dukkanin musulmi, wanda kuma ita ce hakikanin koyarwar manzon Allah (SAWW) wadda ya dora al’ummar musulmi a kanta, kuma ahlul bait (AS) wadanda su ne masu bayyana wa musulmi hakikanin koyarwar manzon Allah suka ginu kai.

3653251


captcha