IQNA

MDD: Wannan Ba Lokaci Da Ya Dace Kabilar Rohingya Su Koma Myanmar Ba

21:04 - February 15, 2018
Lambar Labari: 3482399
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Myanmar ta ki barin musulman Rokhinga komawa gida duk tare da yerjejeniyar da tacimma da kasar Bangladesh kan hakan da kuma bukatar majalisar dinkin duniya na tayi hakan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kwamishinan yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya yana fadawa komitin tsaro na majalisar ta allon bidiyo daga birnin Vienna a jiya talata.

Grandi ya fadawa kwamitin babu wani abu a kasa wanda ya nuna cewa gwamnatin Myanmar zata aiwatar da alakawin da ta dauka. Banda haka har yanzun yan gudun hijira daga yankin Rakhin na kasar ta Myanmar ma suna ci gaba da kwarara zuwa kasar Bangaladesh, don kaucewa hare-haren sojojin kasar.

Kwamishinan ya kara da cewa a cikin watan Fabrairu da muke ciki yan gudun hijira kimanin dubu da dari biyar suka isa Bangladesh.

Ya kuma kara da cewa a cikin watan Maris mai zuwa ne ruwa zai fara sauka a yankin, don haka akwai barazana ga yan gudun hijira kimani dubu 100 wadanda zaune a yankunan da ake ambaliyar ruwa. Yan gudun hijira musulmi yan kabilar Rohingya kimani dubu dari shida da tamanin da takwas suke samun mafaka a kasar Bangladesh ya zuwa yanzu.

3691600

 

 

 

 

 

captcha