IQNA

An Kara Yawan Adadin Kira’a A Gasar Kur’ani Ta Masar

23:50 - February 18, 2018
Lambar Labari: 3482406
Bangaren kasa da kasa, an kara yawan kira’oin da za  ayi a gasar kur’ani ta duniya  a kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na vetogate.com cewa, Ashraf Fahimi daraktan kula da harkokin gasar kur’ani a ma’aikatar harkokin adini ta Masar ya bayyana cewa, dukkanin wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani ta duniya karo na ashirin da za a gudanar a kasar, dole ne zama suna da kwarewa a kira’oi bakawai.

Yak o shakka babu a wannan karon akwai sabbin canje-canje da za  again a wannan gasa, daga ciki har da wannan tsari na samun kwarewa  akan kiraoi bakawai da aka sani.

Ashraf Fahmi y ace wannan gasar za ta samu halartar wakilai daga kasashe 70 na duniya, da suka hada da na larabawa da na musulmi da kuma wasu daga yankunan turai da Asia.

Za a bayar da kyautar fan miliyan daya na Masar ga duk wanda ya yazo na daya  agasar, kamar yadda kuma za  abayar da wasu kyatuka na musamman ga wadanda suka zo matakai na biyu da na uku.

3692645

 

 

 

captcha