Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, shafin yada labarai na almasa ya habarta cewa, Sayyid Masud Buhuwaija babban daraktan kula da harkokin addini a Gundumar Milah ya bayyana cewa an ware sintim miliyan 125, domin gudanar da ayyua na musammana makarantun kur'ani da cibiyoyin addini a wannan gunduma.
Ya ci gaba da cewa, daga cikin wadannan kudi za a samar da tebura dubu 2 sai kuma kujeru 4, da kuma allunan rubutu guda 155, kuma za a raba su a makarantu 14 da kuma cibiyoyi da suke damfare da masallatai 214 a wannan gunduma.
Haka nan kuma ya ci gaba da cewa, sauran kudin za a yi amfani da su wajen taimaka ma kanan makarantu na kur'ani da kuma dalibai da kuma malamai masu bukatar taimako.