IQNA

Majalisar Isra'ila Za Ta Kada Kuri'a Kan Dokar Hana Kiran Salla

22:54 - February 21, 2018
Lambar Labari: 3482417
Bangaren kasa da kasa, Majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra'ila za ta kada kuri'a kan daftarin kudirin hana kiran salla a yankunan Palastinawa da suka hada har da birnin Quds.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, Shafin yada labarai na Nashra ya habarta cewa, majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra'ila ta Knesset za ta kada kuri'a kan daftarin kudirin hana kiran salla a yankunan Palastinawa da suke kusa da matsugunnan yahudawa 'yan share wuri zauna.

Daga cikin wuraren da wannan lamari zai shafa har da yankunan gabashin birnin Quds, bisa hujjar cewa akwai wasu matsugunnan yahudawa a kusa da wasu masallatai na yankin.

Tuna  shekarar da ta gabata ce dai aka gabatar da wannan daftarin kudiri bisa hujjar cewa, kiran salla yana damun yahudawa, musamman a lokacin sallar asubahi, wanda hakan yasa aka gabatar da wannan daftarin doka, idan kuma aka amince da shi, to hakan zai shafi masallatai kimanin 500 a cikin yankunan palastinawa da suke makwaftaka da matsugunnan yahudawa.

3693315

 

 

 

captcha