IQNA

Musulma Ta Kirkiro Wata Kafar Sadarwa Ta Yanar Gizo A Amurka

23:43 - October 22, 2018
Lambar Labari: 3483066
Bangaren kasa da kasa, Laila Alawa wata musulma ce da ke zaune a kasar Amurka wadda ta samar da wata hanyar sadarwa ta yanar gizo a kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na yanar gizo na About Islam cewa, Laila Alawa wata musulma ce ‘yar asalin kasar Syria da ke zaune a kasar Amurka, wadda ta samar da wata hanyar sadarwa ta yanar gizo mai suna The Tempest a kasar Amurka.

Wannan musulma dai wadda ta karanci ilimin sanin halayyar dan adam a jami’a, ta mayar da hankali wajen samar da wata hanyar sadarwa mafi sauri ta hanbyar yanar gizo, domin amfanin mata musulmi a Amurka da ma sauran kasashen duniya, musamman na turai.

Bababr manufar hakan dai ita ce wayar da kan mata musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba, kan muhimmancin kiyaye mutuncin mace ba tare da la’akari da addini ka kabilarta ba, wanda hakan yan ada nasaba ne da irin cin zarafi da mata musulmi suke fuskanta akasashen da ban a muuslmi ba.

A kowace rana miliyoyin mata ne suke kallon abubuwan da take sakawa, da kuma tattaunawa da take yi da daruruwan masana a bangarori daban-daban a kan batutuwa daban daban na ilimi, wanda miliyoyin mata musulmi suke amfana da su, kamar yadda hatta wasu matan da ba musulmi suna amfana da abubuwan da take bayani a  kansu, duk kuwa da cewa ta kan buga misalai da dama kan koyarwar musulunci kan muhimmancin matsayin mata a cikin al’umma da kuma wajabcin kare hakkokinsu a cikin rayuwar zamantakewa.

3758020

 

captcha