IQNA

Bukaci Jami'an Hukumar FBI Ta Amurka Da Su Saki Marzieh Hashemi

22:46 - January 16, 2019
Lambar Labari: 3483317
Hukumar radio ta talabijin ta kasar Iran ta kirayi hukumar tsaro ta FBI a kasar Amurka da ta saki Marzieh Hashemi da suke tsare da ita ba tare da wani laifi ba.

Kamfanin dillancin labaraniqna, Shugaban bangaren watsa watsa shirye-shirye zuwa kasashen ketare na hukumar radio da talabijin ta kasar Iran shi ne ya yi wannan kira, inda ya ce za su ci gaba da bin kadun kame Marzieh ta hanyoyin da suka dace.

Jami'an tsaro na hukumar FBI a kasar Amurka, sun kama ma'aikaciyar tashar Presstv ta kasar Iran Marzieh Hashemi, wadda 'yar kasar Amurka ce musulma da take aiki a Iran kuma tana auren wani dan kasar ta Iran mazaunin birnin Tehran.

Ta isa kasar Amurka ne da nufin ziyartar dan uwanta da ba shi da lafiya, da kuma ziyaratar sauran danginta.

Yanzu haka babu wani wanda yake da masaniya kan halin da take ciki tun bayan kame ta kwanaki biyu da suka gabata, kuma FBI ba ta bayyana wanidalili na kama ta ba.

3781699

 

captcha