IQNA

UNESCO: Sake Gina Birnin Mosil Abu Ne Mai Wahala

22:49 - January 16, 2019
Lambar Labari: 3483318
Babbar darakta ta hukumar raya ilimi da al'adu da wuraren tarihi ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta bayyana cewa, sake gina birnin Mosil na Iraki abu ne mai wahala.

Kamafanin dilalncin iqna, tashar talabijin ta Sky News ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da take gabatar da wani jawabi a birnin Madrid na kasar Spain, babbar darakta ta  hukumar ta UNESCO Audrey Azoulay, ta bayyana cewa hukumar na bukatar ganin an sake gina birnin Mosil saboda muhimmancin da yake da shi ta fuskar tarihi, amma ga dukkanin alamu hakan ba a bu ne mai yiwuwa cikin sauki ba.

Ta ce sun fara aiki a matakin farko, na duba irin asarorin da aka samu a abirnin a lokacin da mayakan 'yan ta'adda na daesh suka kwace iko da birni, da kuma irin barnar da suka yi kafin a fatattake su, inda a halin yanzu UNESCO ta hada kudi kimanin dala miliyan 100 domin fara wannan aiki.

'Yan ta'addan wahabiyawa na Daesh daga kasashen duniya suka shiga cikin kasar Iraki dauke da manyan kayan yaki, inda suka kwace iko da Mosil ne tuna  cikin shekara ta 2014, tare da taimakon wasu kasashen larabawa da suke makwabtaka da Iraki, da nufin kifar da gwamnatin Maliki, da kuma rusa kasar ta Iraki bisa dalilai na bangaranci da babbancin mahanga ta akida.

A cikin watan Yulin 2017 ne dakarun gwamnatin Iraki da sojojin sa kai na kabilun larabawan kasar, da kuma taimakon kasar Iran, suka samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan daga birnin Mosil, tare da sake dawo da doka da oda  abirnin, bayan 'yan ta'adda sun kafa abin da suke kira daular musulmunci, suna kisan jama'a dare da rana.

3781719

 

captcha