IQNA

Daga Farkon 2019 Zuwa Yanzu Isra’ila Ta Kame Falastinawa 2800

21:58 - July 16, 2019
Lambar Labari: 3483848
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni sun tabbatar da cewa daga farkon shekara ta 2019 ya zuwa Isra’ila ta kame falastinawa 2800.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama suka fitar kan yanayin falastinawa da Isra’ila ta kame, an bayyana cewa daga farkon wannan shekara ya zuwa yanzu adaddin ya kai dubu biyu da dari takwas, yayin da 445 daga cikinsu kananan yara, da kuma mata 76.

Rahoton ya ce ya zuwa karshen watan Yunin da ya gabata adadin falastinawan da Isra’ila take tsare da sua  cikin gidajen kaso sun kai 5500, yayin da kimanin 500 daga cikinsu har yanzu ba a yi musu hukunci ba.

Baya ga haka kuma sakamakon mummunar mu’amala da jami’an tsaron Isra’ila suke yi wa wadanan falastinawa, wasu 7 daga cikinsu sun shiga yajin cin abinci.

Daga farkon shekara ya zuwa yanzu, Isra’ila ta sake kame wasu falastinawa 17 daga cikin wadanda ta saka daga gidan kaso.

3827398

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha