IQNA

Shiri A Gidan Radiyon Uganda Kan Mahangar Imam Khomeini kan Annabi Isa (AS)

19:55 - December 28, 2018
Lambar Labari: 3483257
Bangaren kasa da kasa, a jiya ne aka gudanar da wani shirin a gidan radiyon Kampala a kasar Uganda kan mahangar marigayi Imam Khomeni dangane da annabi Isa (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna, karamin ofishin jakadancin Iran a  Uganda ya dauki nauyin shirin wanda aka gudanar a gidan radiyon Kampala a kasar ta Uganda kan mahangar marigayi Imam Khomeni dangane da annabi Isa (AS) a mahanga ta ilimi da kuma darussa.

Shugaban karamin ofishin jakadancin an Iran a Uganda shi ne ya gabatar da bayanin a cikin shirin, inda ya kawo bayanai da dama da Imam khomeni ya yi a kan annabi Isa da kuma abubuwan da ya rubuta a cikin littafansa daban-daban.

Marigayi Imam Khomeni yana bayyana annabi Isa (AS) a matsayin wata babbar ayar ubangiji, kamar yadda kur’ani mai tsarki yake siffanta shi, domin kuwa Allah madaukakin sarki ya nuna ayoyinsa dangane da sha’anin annabi Isa (AS) tun daga lokacin haihuwarsa har zuwa lokacin aiko shi da annabta.

Baya ga haka kuma a lokacin da aka aiko shi da sako na manzanci ga al’umma, ya zo da ayoyi masu girma wadanda suka zama muujiza ta annabatarsa, kamar warkar da makafi da raya matattu da sauran abubuwa makamantan wadannan da yayi da iznin Allah madaukakin sarki.

Haka nan kuma wata babbar ayar ita ce yadda Allah ya kubutar da shi daga shirtin yahudawa da suka nemi kasha shi, inda har yanzu yake raye, kuma zai dawo domin isar da sako na Allah, domin tabbatar da tauhidin Allah da kuma tabbatar wa duniya cewa shi bawan Allah ne kuma manzonsa.

3776029

 

 

 

 

captcha