IQNA

Shugaba Rauhani: Dole Ne A warware Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Ta Hanyar Tattaunawa

23:21 - October 13, 2019
Lambar Labari: 3484148
Bangaren siyasa, a lokacin da yake zantawa da firayi ministan Pakistan a yau shugaba Rauhani ya ce dole a warware matsalolin gabas ta tsakiya ta hanyar tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau ne piraministan kasar Pakistan Imran Khan ya iso birnin Tehran a wata ziyarar aiki, inda ya gana da shugaban kasar Iran Hassan Ruhani, a lokacin taron manema labarai da suka gudanar tsakaninsu Imran Khan ya bayyana cewa kasarsa za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an tattauna tsakanin Iran da Saudiyya, domin bamajin dadin yadda ake samun zaman tankiya tsakanin kasashen biyu, don hakainafarinciki sosai wajen ganin an budekofar tattaunawa tsakanin Iran da Saudiya,

Ana shi bangaren shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya fadi cewa suna maraba da duk wani yunkuri na alheri, kuma mun yi amanna cewa ta hanyar tattaunawa ce kawaizaa iya warware rikicin yankinda kum bin hanyar diplomsiya da tattaunawa tsakanin kasashen yanki,

ziyarar ta Pita minstan Pakistan za ta mayar da hankali ne kan batutuwan zaman lafiya da tsaro a yankin, kuma ita ce ziyara ta 2 a irinta da ya kawo birnin Tehran a wannan shekarar, a dai dai lokacin da alamra ke kara zafi a yankin, kuma ana sa ran zai gana da jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahi Khamna’I , zuwa ranar Talata kuma zai wuce kasar Saudiya.

 

3849655

 

 

 

 

 

 

 

captcha