Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke kula da lamurran hubbaren Imam Ali A Najaf Ashraf ta sanar da cewa a wanann shekara ba za a gudanar da tarukan ranar Ghadir a wannan hubbaren ba kamar yadda aka a kowace shekara.
Bayanin ya ci da, an dauki wannan matakin ne sakamakon yanayin da aka samu kai a wannan lokaci na bullar cutar corona, domin kare lafiya dukkanin mumiminai maso Amirul muminin daga kamuwa da wannan cuta wadda take yaduwa, ya zama wajibi a dauki irin wannan mataki.
Daga karshe bayanin ya nemi afuwar dukkanin wadada suka yi niyyar halartar wadannan taruka a shekarar bana.
A birnin karbala ma an bayar da sanarwar cewa an dakatar da duk wasu taruka daga nan har zuwa bayan 13 ga watan Muharram.