IQNA

Musulunci A Kasar Afirka Ta Kudu Tun Daga Lokacin Isar Sheikh Yusuf A kasar

22:44 - May 02, 2021
Lambar Labari: 3485867
Tehran (IQNA) muslunci ya isa kasar Afirka ta kudu ne tuna cikin karni na goma sha bakawai lokacin da sheikh Yusuf ya isa kasar

Addinin muslunci ya isa kasar Afirka ta kudu ne tuna cikin karni na goma sha bakawai lokacin da sheikh Yusuf ya isa kasar, wanda ya kasance aga cikin wadanda suka yi hijira daga yankuna daban-daban na gabashin India da kuma Indonesia zuwa kasar Afirka ta kudu a ciki karnin na 17 miladiya.

Ya isa yankin Capetown, daga lokacin ne kuma ya gina masallaci an farko a kasar Afirka ta kudu, kuam ya ci gaba da yin kira zuwa ga addinin muslunci.

Musulunci A Kasar Afirka Ta Kudu Tun Daga Lokacin Isar Sheikh Yusuf A kasar

Turawan Holland da suke a kasar lokacin ba su nuan masa wata tsangwama ba, wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da fadada ayyukansa na yada addinin muslucni a yankin.

Wannan ne yasa mutanen kasar Afirka ta kudu suke kiran Sheikh Yusuf da baban addinin muslunci a kasar, domin kuwa shi ne wanda ya fara gina masallaci a kasar tare da kiran mutane zuwa ga addinin muslunci.

Kasar Afirka ta kudu na daga cikin kasashe wadanda akasarin mazauna kasar mabiya addinin kirista ne, amma kuma msuulmi suna da matsayi da ake girmama su a kasar, kasantuwar musulunci ya shiga kasar tun daruruwan shekaru da suka gabata.

 

3968390

 

 

 

captcha