IQNA

Wata Cibiyar Musulmi A Burtaniya Ta Samu Lambar Yabo Ta Sarauniyar Kasar

23:38 - June 05, 2021
Lambar Labari: 3485985
Tehran (IQNA) wata kungiyar musulmi a kasar Burtaniya da ke gudanar da ayyukan jin kai da taimako ta samu lambar yabo daga sarauniyar kasar.

Jaridar The National News ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, kungiyar musulmi ta The Muslim Arts and Culture Festival a kasar Burtaniya da ke gudanar da ayyukan jin kai da taimako ta samu lambar yabo daga sarauniyar kasar ta Burtaniya.

Sakatariyar ma'aikatar kula da harkokin zamantakewar al'ummar kasa a Burtaniya Barones Barran ta bayyana cewa, an bayar da wannan kyauta ne ga wannan kungiya, saboda gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen taimakon jama'a a lokacin da cutar corona ta yi tsanani a kasar.

Wannan cibiyar dai  tana gudanar da ayyukanta ne a birnin Manchester, wanda shi ne birnin na uku mafi girma a kasar Burtaniya.

Daga cikin ayyukan da wannan cibiya take gudanarwa har da taimaka ma marassa karfi da abubuwan bukatar rayuwa, taimaka musu a asibitoci, kamar yadda kuma tana shirya taruka na wayar da kai domin kawp karshen nuna wariyar launin fata, ko kin jinin musulmi da dai sauransu.

 

3975519

 

captcha