IQNA

Dubban Yahudawa Sun Gudanar Da Jerin Gwano Domin Neman A Hukunta Netanyahu

20:45 - June 15, 2021
Lambar Labari: 3486013
Tehran (IQNA) dubban yahudawan Sahyuniya sun gudanar da jerin gwano a biranan Tel Aviv da Quds domin neman a hukunta Netanyahu.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya dubban yahudawan Sahyuniya sun gudanar da jerin gwano a biranan Tel Aviv da Quds domin neman a hukunta tsohon firayi ministan Isra’ila Netanyahu kan manyan laifukan da ya aikata.

Wannan na zuwa ne dai bayan da Naftali Bennett da abokin kawancensa Lapid suka samu amincewar majalisar Knesset ta Isra’ila kan kafa sabuwar gwamati, bayan da Netanyahu ya kasa.

Yaudawan masu jerin gwano sun bukaci bangaren shari’a da ya gurfanar da Netanyahu kan laifukan cin ahnci da rashawa da kuma halasta kudaden haram da zamba cikin aminci da ya yi a lokacin da yake rike da kujerar firayi ministan Isra’ila.

Sai dai a nata bangaren kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta bayyana cewa, babu bambanci tsakanin gwamnatin Netanyahu da kuma duk wata gwamnati da aka kafa a Isra’ila, domin kuwa duk bisa siyasa daya aka kafa su.

Fauzi Barhum mai magana da yawun kungiyar Hamas ya bayyana cewa, manufar siyasar Isra’ila ta ginu ne kan mamayar yankunan Falastinawa da kuma danne hakkokinsu bisa zalunci, wanda kuma Falastinawa masu lamiri ba za su tana amincewa da haka ba.

3977511

 

 

captcha