IQNA

Jagoran Juyi Na Iran: Fitowa Zabe Ke Fayyace Makomar Kasa Da Tsarin da ta Ginu A Kansa

22:39 - June 16, 2021
Lambar Labari: 3486018
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana fitowar al’umma a zabuka a matsayin abin da yake fayyace makomarta.

A jawabin da ya gabatar a yammacin yau, Jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, fitowar al’umma a zabuka ita ce ke fayyace makomarta da kuma tsarinta.

Jagoran ya gabatar da wannan jawabi ne kasa da sa’o’i 48 kafin fara gudanar da zabukan shugaban kasa da na kananan hukumomi a fadin kasar Iran, wanda zai gudana a ranar Juma’a mai zuwa.

A cikin jawabin nasa, jagoran ya bayyana cewa, tun daga lokacin da aka yi juyin juya halin muslunci a Iran, al’umma ne da kansu suke tafiyar da kasarsu ta hayar zabe, domin kuwa tun daga farkon juyin, an fara ne da gudanar da zaben raba gardama kan irin tsarin da zai tafiyar da kasar, inda fiye da kashi 98% na mutanen kasar ne suka zabi tsarin musulunci ya zama shi ne tsarin da za a kafa gwamnati a kansa.

Ya ce tun daga wancan lokacin ne kuma manyan kasashen duniya masu girman kai suka fara nuna kiyayya ga duk wani da ya shafi zaben kasar Iran, kuma har yanzu wannan salon nasu bai canja, ta yadda ba su kallon ra’ayin al’ummar Iran a matsayin ra’ayi mai kima, balantana su yi  la’akari da shi a matsayin cewa shi ne yake fayyace makomar kasar.

A daya bangaren kuma ya kirayi jami’an da suke shirya zabukan da su sauke nauyin da ya rataya a kansu, na shirya zabe kamar yadda ya kamata tare da kiyaye hakkokin kowane dan takara, da kuma kiyaye hakkoin masu zabe, tare da samar da kyakkyawan tsari wajen gudanar zaben, da kuma kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya, musamman a wannan lokaci.

 

3978035

 

captcha