IQNA

Ministocin Al’adu Na Kasashen Musulmi Za Su Gudanar Da Zama A Oman

17:08 - October 22, 2015
Lambar Labari: 3391739
Bangaren kasa da kasa, ministoci masu kula da harkokin al’adu a kasashen musulmi na (ISESCO) za su gudanar da wani zama a birnin Maskat fadar mulkin kasar Oman.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jamhuriyar muslunci cewa, wannan zaman taro dai za a gudanar da shi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin al’adu ta kasar Oman, domin duba ci gaban da aka samu a wannan bangare.

A wannan taro dai ministocin ma’aikatun kula da harkokin al’adu na kasashen larabawa da na musulmi da ma wasu kasashe da aka gayyata za su samu halarta.

Zaman dai zai mayar da hankali wajen yin dubi dangane da yadda kasashen yammacin turai suke mayar da hankali wajen yin farfaganda a kafofin yada labaransu dangane da yadda kasashen musulmi suke ta fuskar al’adu da sauransu.

Bisa la’akari da yadda a kowane lokaci musamamn a cikin shekarun na kafofin yada labarai na kasashen turai suka mayar da hankali matuka kan abubuwan da suke faruwa na ta’addanci da sunan musulunci, wannan yana yin mummunan tasiri a cikin zukatan wasu.

Wannan ne yasa wasu daga cikin mambobin kungiyar ta ISESCO kiran zaman taro domin duba hanyoyin da ya kamata  abi domin fuskantar wannan lamari mai matukar hadari.

Abin tuni a nan dai shi ne a gefen taro, za a zabi birnin Nuzui a cikin gundumar Dakhiliyyah ta kasar Oman a matsayin birnin al’aduin muslunci na shekara ta 2015.

3391363

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha