IQNA

Jagora: Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Ha'inci Almomin Musulmi Da Na Falastinawa Kan Kulla Hulda Da Isra'ila

22:55 - September 01, 2020
Lambar Labari: 3485139
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ce UAE ta ha’inci kasashen musulmi ta hanyar kula hulda da Isra'ila.

Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa gwamnatin Hadaddiyar daular Larabawa UAE ta ha’inci kasashen musulmi da kuma alummar Falasdinu saboda maida huldar jakadanci da Haramtacciyar kasar Isara’ila da ta yi. Sannan ya kara da cewa, wannan halin ba zai da de ba.

Jagoran ya bayyana hakan ne a safiyar yau Talata, a lokacin da ya ke jawabi a taron hotunan badiyo da jami’an ma’aikatar ilmi da tarbiyya ta kasa a nan Tehran.

Ya ce; Lalle wannan halin ba zai dore ba, kuma kunya zaya wanzu a faskar wadanda suka yi watsi da mamayar Falasdinu da kuma falasdinawa, wadanda aka kora daga gidajensu, sannan suka bawa Isra’ila damar fadada ikonta a yankin” in ji jagoran.

Daga karshe jagoran ya bukaci gwamnatin Hadaddiyar daular Larabawa ta farka kafin lokaci ya kure mata, ta kuma yi abinda ya dace.

Dangane da tsarin tarbiyya da ilmi a kasar Iran kuma, Jagoran ya bayyana cewa kasashen yamma sun dage sai sun kutsa cikin tsarin tarbiyya da ilmi na kasashen duniya, musamman na kasar Iran, ta kudurin majalisar dinkin duniya.

Haka nan kuma jagoran ya kara da cewa tsarin tarbiyya, wanda kasashen yamma suke bi a halin yanzu, ya rika ya karye, domin baya iya samar da nagartacciyar tarbiyar da ake butakata a duniya.

 

3920299

 

 

captcha