IQNA

OIC Ta Gudanar Da Zama Kan Halin Da Musulmin Rohingya Suke Ciki

22:43 - January 27, 2021
Lambar Labari: 3485594
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen musulmi ta gudanar da zama domin tattauna halin da musulmin Rohingya suke ciki.

Kamfanin dillancin labaran BANA ya bayar da rahoton cewa, a yau Laraba kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta gudanar da zama domin tattauna halin da musulmin Rohingya na kasar Myanmar suke ciki.

Taron wanda aka gudanar ta hanayar yanar gizo, ya samu halartar wakilan kungiyar ta kasashen musulmi da kuma jami’an hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, gami da wakilan kwamitoci daban-daban da suke aiki dangane da batun musulmin na Rohingya.

Samir Bakar mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen musulmi, kuma wakilin kungiyar kan lamurra ad suka shafi lamurran al’ummar falastinu ya bayyana cewa, batun musulmin Rohingya batu ne na ‘yan adamtaka a mataki na farko, sannan kuma ga dukkanin musulmi batu na ‘yan uwantaka.

Ya ce nauyi ne da ya rataya a kan kungiyar kasashen musulmi da kuma majalisar dinkin duniya, kula da wadannan bayin Allah da aka tagayyara su, tare da samar musu da dukkanin abin da ya sawaka domin taimakon rayuwarsu.

A daya bangaren kuma wakilin kungiyar kasashen musulmi kan lamurra da suka shafi musulmin Rohingya Ibrahim Khairat ya bayyana cewa, suna gudanar da dukkanin ayyukan da suka kamata a bangaren taimakon muuslmin Myanmar, tare da tabbatar da kare hakkokinsu a cikin kasarsu.

 

3950372

 

captcha