IQNA

Akwai Yiwuwar Barkewar Cutar Kwalera A Cikin Musulmin Rohingya

23:34 - September 02, 2017
Lambar Labari: 3481858
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana tsananin damuwarsa dangane da ci gaba da take hakkokin musulmin Rohingya na kasar Myammar da mahukuntan kasar suke yi wanda hakan na kara sanya musulmin cikin mawuyacin hali.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habata cewa, kammafanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan irin mawuyacin halin da musulmin kasar Myammar din suke ciki inda ya bukaci jami'an tsaron kasar Myammar din da su nesanci ci gaba da abubuwan da suke yi wanda zai kara sanya musulmin cikin mawuyancin hali.

Rahotanni daga kasar Myammar din suna nuni da cewa sakamakon karin sojoji da gwamnatin Myammar din ta tura jihar Rakhine a farko-farkon watan Agustan da ya gabata, gwamnatin ta kara irin dirar mikiyan da take yi wa musulmin Rohingya din na kasar lamarin da ya tilasta wa dubun dubatan musulmin guda daga garuruwansu zuwa kasar Bangladesh da ke makwabtaka da su.

Kasashe da cibiyoyin kasa da kasa dai suna ci gaba da Allah wadai da irin wannan zaluncin da gwamnatin Myammar din da kuma 'yan daban mabiya addinin Budha da suke samun goyon bayan gwamnatin suke yi wa musulmin kasar.

3637110


captcha