IQNA

Guterres Ya Yi Allawadai Da Harin Ta’addanci Da Aka Kai A Kasar Somalia

23:28 - February 02, 2021
Lambar Labari: 3485613
Tehran (IQNA) Babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi Allawadai da harin da aka kaddamar a birnin Mogadishu na kasar Somalia.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, kakakin babban sakataren majalisar dinkin duniya Stephen Dujarric ya bayyana cewa, Antonio Guterres ya bayyana cewa takaicinsa matuka dangane da abin day a faru na harin da aka kai birnin Mogadishu.

Yace abin da ya faru abin bakin ciki ne kuma abin da ya kamata a yi Allawadai da shi ne, kuma majalisar dinkin duniya tana nan kan bakanta na taimaka ma gwamnatin kasar Somalia.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai aka kai hari da bama-bamai a kan babban otel din Afrik da ke birnin Mugadishu, jim kadana bayan tashinsu kuma wasu masu dauke da makamai su uku suka kutsa kai cikin otel din suka bude wuta kan jama’a.

Jami’an tsaro sun ce mutane 9 ne suka rasa rayukansu da suka hada da mutane hudu da suka kai harin, wasu da dama kuma sun samu raunuka.

Otel din da aka kai ma harin dai a nan manyan jami’an gwamnatin kasar suke sauka, a nan kuma ake gudanar da mafi yawan taruka da suka shafi gwamnati.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Alshab ta sanar da cewa it ace take da alhakin kai harin.

3951481

 

captcha