IQNA

An Bude Kofa Ga Masu Ziyara A Birnin Najaf Na Iraki

23:10 - July 17, 2021
Lambar Labari: 3486114
Tehran (IQNA) an bude kofa ga masu gudanar da ayyukan ziyara a birnin Najaf na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, Hassan Nazem ministan al'adu da yawon bude ido na kasar Iraki ya bayyana cewa, an bude kofa ga masu gudanar da ayyukan ziyara a birnin Najaf na kasar Iraki, bayan daukar matakan da aka yi a baya saboda cutar corona.

Ya ce duk da cewa a halin yanzu bude kofa ga masu ziyara daga ko'in a cikin fadin duniya, amma akwai matakai wadanda ake dauka wadanda dole ne a kiyaye su.

Daga cikin matakan har da tabbatar da cewa dukkanin masu ziyara da suke shigowa sun cika ka'idoji na kiwon lafiya, daga cikin har da tabbatar da cewa suna dauke da ingantattun takardun shedar gwajin corona, da ke tabbatar da cewa ba su dauke da cutar kwanaki uku kafin shiga kasar Iraki.

Baya ga haka kuma dole ne masu ziyara su kiyaye dukkanin ka'idoji na saka takunkumin fuska, da kuma kula da tsafta da bayar da tazara.

 

 

3984723

 

captcha