IQNA

Matsin Lambar Saudiyya A Kan Lebanon Ba Zai Amfanar Da Kowa Ba Sai Makiya Musulunci

19:56 - October 31, 2021
Lambar Labari: 3486496
Tehran (IQNA) kungiyoyi da jam'iyyun siyasa da malaman addini a Lebanon suna bayyana cewa matsin lambar Saudiyya kan kasar ba zai amfanar da kowa ba sai Amurka da Isra'ila.

A cikin jawabai da sakonni daban-daban da suka fitar, kungiyoyi da jam'iyyun siyasa da malaman addini a Lebanon suna bayyana cewa matsin lambar Saudiyya kan kasar ba zai amfanar da kowa ba sai Amurka da Isra'ila.

A nata bangaren ita ma Kungiyar Hizbullah ta kasar ta Lebanon ta bayyana yunkurin Saudiyya na yin matsin lamba kan kasar Lebanon da cewa hidima ce ga makiya, kuma hakan ba zai amfanar da masarautar Al saud da komai ba illa kaskantar da kanta a gaban makiya muslunci da musulmi.

Baya ga haka kuma kungiyar  ta ce babu wani abin jayayya a cikin kalaman ministan yada labaran Lebanon, inda ya ce yakin da Saudiyya ke jagoranta kan al'ummar kasar Yemen bai dace ba kuma wauta ce, kuma wannan ita ce matsaya ta dukkanin larabawa da musulmi masu 'yanci, wanda kuma duk wannan kumfan bakin da iyalan gidan sarautar Al Saud suke yi kan Lebanon a kan wannan maganar ne.

Wasu da dama dai suna ganin cewa, Saudiyya ce da kanta ta bankado wannan tsohuwar magana kuma ta mayar da ita abin tayar da jijiyoyin wuya tsakaninta da Lebanon, domin ta kawar da hankulan al’ummomin duniya kan batun tonon sililin da tsohon babban jami’in hukumar leken asirin kasar ta Saudiyya Saad Al-jabri ya yi a makon da ya gabata daga kasar Canada, wanda ya bayyana cewa Muhammad Bin Salman ya yi yunkurin kashe marigayi sarki Abdullah a lokacin yana kan mulki, domin ubansa Salman ya dare kan kujerar sarautar kasar Saudiyya.

Kafin Saudiyya ta samo abin da za ta yi kumfan baki a kansa domin kawar da hankulan duniya akan wannan tonon silili, ta fara saka gidauniyar Qard Al-hassan ne a cikin kungiyoyin ta'addanci, cibiyar da ke karkashin Hizbullah, wadda kuma take bayar da tallafi ga mabukata domin rage radadin talauci a kasar Lebanon.

Bangarori daban-daban a kasar ta Lebanon masu 'yancin siyasa da kuma lamiri, sun yi tir da Allawadai da wannan matsaya ta gwamnatin Al saud, tare da bayyana hakan a matsayin shigar shugula a cikin harkokin Lebanon, kuma hakan yana matsayin hidima ne ga makiya al'ummar musulmi da na larabawa wato Amurka da yahudawan Isra'ila, wadanda masarautar Al saud ke hankoron ganin ta faranta musu rai ko ta wane hali domin su ba ta kariya da tsari.

Bayan daukar wannan matakin da masarautar Al saud tana matsa lamba kan Lebanon har da korar jakadan Lebanon da ke birnin Riyad, da kuma kiran jakadanta da ke Beirut, wasu daga cikin gwamnatocin kasashe masu yi ma Masarautar Al saud amshin shata daga cikin kasashen larabawa musamman Bahrain da hadaddiyar daular Larabawa, sun dauki irin wannan mataki kamar yadda suka saba yin hakan a kowane irin lamari da masautar Al Saud ta dauki matsayi a kansa.

 

4009459

 

 

captcha