IQNA

Rugujewar masallaci mafi dadewa a yankin Anadolu a girgizar kasar da ta auku a baya bayan nan

18:08 - February 12, 2023
Lambar Labari: 3488648
Tehran (IQNA) Masallacin Habib Najar wanda shi ne masallaci mafi dadewa a yankin Anatoliya kuma ya samo asali ne tun farkon tarihin Musulunci, ya ruguje gaba daya a girgizar kasar da ta afku a makon jiya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Middle East Eye cewa, girgizar kasa mai karfin awo 7.8 da ta afku a kasashen Turkiyya da Siriya a makon da ya gabata ta shafi mutane sama da miliyan 23. Adadin wadanda suka mutu ya zarce 20,000, dubun dubatar sun jikkata, kuma an bar mutane da dama ba su da matsuguni.

Wannan girgizar kasar ta kuma lalata muhimman wuraren tarihi da na dadadden tarihi a kasashen Siriya da Turkiyya. A Siriya, an lalata wani tsohon kagara a Aleppo. A Gaziantep, Turkiyya, wani sanannen katafaren gidan da ya tsaya sama da shekaru 2000 ya zama kango. Daga cikin barnar da aka yi wa kayayyakin tarihi na Turkiyya har da Masallacin Habib Najar, wanda ke da shekaru dari da dama, kuma yana Antakiya, daya daga cikin garuruwan da aka lalace.

Hotunan wannan masallacin da aka yada a yanar gizo sun nuna cewa kurbar masallacin ta ruguje gaba daya inda wurin ya rikide ya zama tarkace.

Wannan masallaci shi ne masallaci mafi dadewa a yankin Anatoliya. An ciro sunan wannan masallaci daga Habib Najar, wanda aka ce ya rayu a wancan zamanin kuma ya yi imani da koyarwar Yesu Almasihu. Wannan masallaci mai tarihi ya kasance muhimmin abin jan hankali ga masu yawon bude ido.

 

4121462

 

captcha