IQNA

Karim Benzema yana ziyartar dakin Allah

16:00 - August 07, 2023
Lambar Labari: 3489605
Makkah (IQNA) Tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa mai suna Karim Benzema a kungiyar Ittihad ta kasar Saudiyya ya ja hankalin masoyansa inda ya buga wani faifan bidiyo a masallacin Harami a lokacin da yake gudanar da aikin Umrah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Masrad cewa, Karim Benzema tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa na kungiyar Al Ittihad ta kasar Saudiyya ya wallafa wani faifan bidiyo na kansa yana aikin Umrah kwana guda bayan fitar da wannan kungiya daga gasar kungiyoyin ta Saudiyya.

Benzema ya wallafa wannan bidiyo ta shafin sa na Instagram, A cikin wannan faifan bidiyon, yana dawafi a dakin Ka'aba yana cewa a cikin harshen Faransanci: "Gaskiya daya tilo..." Alhamdulillah.

A baya dai shahararren dan wasan nan dan kasar Faransa a fagen kwallon kafa a duniya ya bayyana farin cikinsa na taka leda da zama a kasar Musulunci.

An fitar da Al-Ittihad ne bayan ta sha kashi a hannun Al-Hilal da ci 3-0 a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar zakarun kungiyoyin Saudiyya da aka fi sani da gasar cin kofin Sarki Salman.

 

 

 

 

captcha