IQNA

Taron kur'ani mai tsarki na maulidin Sayyida Zahra (AS)

19:40 - January 02, 2024
Lambar Labari: 3490410
Najaf (IQNA) cibiyar hubbaren Imam Ali ta sanar da gudanar da taron kur'ani mai tsarki tare da halartar gungun makarantun kasar Iraki da na kasashen duniya a daidai lokacin da aka haifi Sayyida Fatima Zahra (AS) mai albarka.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, an gudanar da taron kur’ani mai tsarki tare da halartar gungun makarantun kasar Iraki da na sauran kasashen duniya a daidai lokacin da aka haifi Sayyida Fatima Zahra (AS) mai albarka.

Haider Rahim, shugaban sashen yada labarai na hubbaren ya bayyana cewa: Wannan bikin ya kunshi abubuwa da dama da ayyuka da suka fara a ranar Litinin da ta gabata kuma za su ci gaba har tsawon mako guda.

Ya kara da cewa: Wadannan ayyuka za su fara ne da gudanar da taron kur'ani mai tsarki a farfajiyar Alawi mai alfarma tare da halartar manyan malamai da zababbun masu yabo daga kasar Iraki da ma wajen kasar.

Haka kuma wannan biki zai kunshi abubuwa da dama da suka hada da taron majalisar karatu na Al-Rawdah Al-Haydriya da gudanar da tarukan da suka shafi mata, da kuma wasu ayyuka na mata masu ziyara.​​

 

 

4191257

 

 

 

 

captcha