IQNA

Babban Masallacin Japan Yan wayar Da Kan Mutane Dangane Da Musulunci

23:45 - March 24, 2015
Lambar Labari: 3036055
Bangaren kasa da kasa, Babban masallacin kasar Japan yana gudanar da wasu sabbin shirin na wayar da kan mutane dangane da addinin muslunci na hakika.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Japan News cewa, Domin wayar da kan sauran jama’ar kasar masallacin birnin Tokyo na kasar Japan yana gudanar da wasu sabbin shirye-shirye na wayar da kan mutane dangane da addinin muslunci da kuma hakikanin koyarwarsa.
Wanann y azo ne domin bayar da masaniya ga mutanen kasar wadanda bas u san wani abu dangane da koyarwar muslunci ba, maimakon hakan ma suna kallon wannan addini mai tsarkia  matsayin wani addini mai dake da wata akida maras kyau, wadda ake danganta ta da ta’addanci, kamar dai yadda yake a wasu bangarori na duniya yadda ake kallonsa.
A kan wannan masallacin wanda shi ne mafi girma  akasar, wasdda ke da masallatai kimanin saba’in a fadin kasar baki daya, ya mayar da hankali matuka domin nuna wa jama’a cewa wannan addini na zaman lafiya ne da fahimtar juna ban a ta’addanci ba kamar yadda aka yada wa duniya, da kuma yadda wasu jahilai daga cikin muslumin suke kokarin bayyana wa duniya ta hanyar ayyukansu munana.
3033000

Abubuwan Da Ya Shafa: Japan
captcha